Hukomomin lafiya na kasar Falasdin sun ce akalla Falasdinawa uku aka kashe tare da jikkata wasu sama da 20 a hare-hare ta sama da dakarun Isra’ila suka ƙaddamar kan sansanin ‘yan gudun hijira a yankin jenin da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan da ke ƙarƙashin mamaye.
Wata kafar yada labarai ta rawaito cewa jami’an tsaron Falasdinawa na cewa Isra’ila ce ta ƙaddamar da wani gagarumin samame a yankin, inda aka hango jerin gwanon motocin soja na shiga sansanin, ta kowacce kusurwa.
Ministan tsaron Isra’ila ya ce jami’ansu na aiki tukuru cikin ‘yan sa’o’in da suka wuce, a ƙoƙarin kawar da abin da ya kira “‘yan ta’adda” a Jenin.
Wani direban motar ɗaukar marasa lafiya a Falasɗinu ya bayyana yadda tashin hankali ke ƙaruwa a yankin Jenin na Falasɗinu, wanda ya raunata mutane da dama.
Khaled Alahmad ya faɗa wa kamfanin labarai na Reuters cewa lamarin ya yi “kama da yaƙi”, yayin da hare-haren sojan Isra’ila ke sauka kan sansanonin ‘yan gudun hijira.
Wannan ta sa Jagoran mayaƙan Hamas, Ismail Haniyeh, ya bayyana harin da aka kai wa sansanin da cewa rashin imani ne kuma babu tausayi.