• Home  
  • Shettima Ya Fasa Zuwa Taron Ƙungiyar Ƙasashen Rainon Ingila
- Babban Labari - Labarai

Shettima Ya Fasa Zuwa Taron Ƙungiyar Ƙasashen Rainon Ingila

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Kashim Shettima ya fasa zuwa taron da ƙungiyar ƙasashe rainon Ingila ta Commonwealth na shekarar 2024, da za’a gudanar a tsibirin Samoa. Shettima ya fasa zuwa taron ne saboda matsalar da jirgin sa ya samu a lokacin da ya yada zango a ƙasar Amurka. Mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo […]

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Kashim Shettima ya fasa zuwa taron da ƙungiyar ƙasashe rainon Ingila ta Commonwealth na shekarar 2024, da za’a gudanar a tsibirin Samoa.

Shettima ya fasa zuwa taron ne saboda matsalar da jirgin sa ya samu a lokacin da ya yada zango a ƙasar Amurka.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya ce a lokacin da jirgin ya yada zango a birnin New York, wani abu ya daki jirgin mataimakin shugaban kasar wanda yayi sanadiyyar lalata gilas ɗin direban jirgin.

Sanarwar ta ƙara da cewa tuni dai Shugaba Tinubu ya amince da tura tawagar ministoci, ƙarƙashin jagorancin ministan Muhalli, Abbas Lawal domin su wakilci Najeriya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000