• Home  
  • Babu Ranar Daina Amfani Da Tsoffin Takardun Naira” – CBN
- Babban Labari - Labarai

Babu Ranar Daina Amfani Da Tsoffin Takardun Naira” – CBN

  Babban bankin kasa na CBN, ya yi watsi jita jitar da ke yawo cewa daga ranar 31 ga watan Disamban shekarar nan ta 2024, za’a daina amfani da tsofaffin takardun kudi Na Naira.  Bayanin watsi da jita jitar na zuwa ne a jiya Alhamis, inda babban bankin ya bayyana magana a matsayin mara tushe […]

 

Babban bankin kasa na CBN, ya yi watsi jita jitar da ke yawo cewa daga ranar 31 ga watan Disamban shekarar nan ta 2024, za’a daina amfani da tsofaffin takardun kudi Na Naira. 

Bayanin watsi da jita jitar na zuwa ne a jiya Alhamis, inda babban bankin ya bayyana magana a matsayin mara tushe ballantana makama.

 

A cewar bankin, “bisa hukuncin da kotun kolim Najeriya tayi, a ranar 29 ga watan Nuwamban 2023, ta ce a cigaba da amfani da takardun ba tare da iyakancewa ba” inji sanarwar.

‘Bugu da kari, sanarwar ta yi kira ga bankuna da su cigaba da mu’ amala da tsoffin takardun kudin.

Matakin na zuwa ne kwana daya bayan da majalisar wakilan Najeriya ta yi kira ga CBN da su fara shirye shiryen janye tsaoffin takardun Naira.

A shekarar 2022 ne dai tsohuwan gwamnatin Muhammadu Buhari, ta ɓullo da sabbin takardun kuɗin ƙasar na naira 200, da 500 da 1,000, sannan ta bayar da wa’adin daina amfani da tsoffin zuwa ƙarshen shekarar.

Batun ya haifar da ruɗani da tayar da hankali, inda daga baya wasu jihohin ƙasar suka shigar da ƙara a gaban kotun ƙolin ƙasar, wadda kuma ta jinkirta wa’adin, zuwa wani lokaci, inda daga baya ma ta ce a ci gaba da amfani da su ba tare da iyakancewa ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai