Shettima ya kai ziyara Kwara bayan mummunan harin jihar

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya kai ziyarar jaje zuwa jihar Kwara inda mahara suka kashe gomman mutane cikin makon nan.

Cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar ta ce Shettima ya kai ziyarar ce bisa umarnin shugaban ƙasar Bola Tinubu.

“Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa ya kai ziyarar jaje jihar da kuma duba halin da take ciki tare da miƙa sakon jaje a madadin gwamnatin tarayya,,’ in ji sanarwar.

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ne ya tarbi mataimakin shugaban ƙasar a lokacin ziyarar.

A ranar Talata da daddare ne wasu mahara suka far wa ƙauyen Woro da Nuku da ke yankin ƙaramar hukumar Kaiama tare da kashe fiye da mutum 70.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *