Shugaban kasar Amurka wato Joe Biden ya bayar da lambar yabo ta musamman ga shahararren dan kwallon nan na kasar Argentina Leonel Messi.
Ya bayar da lambar yabon ne a fadar sa ta shugabancin kasar ta Amurka wato White House a wannan rana ta Asabar.
A wannan kadami da ake ciki Leonel Messi ya bar nahiyar Turai da fafata wasa inda ya koma kasar Amurka wato kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami dake kasar.
A wani bangare ma an bayyana cewar Leonel Messi yana da shiyya a wannan kungiya kuma sakamakon komawarsa kasar ta Amurka yanzu haka gasar ta kara samun armashi da kuma mabiya sakamakon kallon wasanninsu da ake yi ta dalilin Messi.
Ita dai wannan kyauta ta lambar yabo itace kyauta mafi kyau da tsada da ake baiwa wani sibiliyan a kasar ta Amurka inda ta tafi ga danwasa Messi.
Amma kash, an samu cikas inda Messi bai samu damar halartar fadar shugaban kasar ba sakamakon gagarumin uzuri da ya bayar.
Joe Biden dai na kokarin ban kwana da wannan fada inda yake kokarin tattara nasa ya nasa domin damkawa Donald Trump mulki bayan da yayi rashin nasara a zaben da ya gabata na kasar ta Amurka.