Shugaban ƙungiyar Izala ta Ƙasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ziyarci mamallakin tashoshin MUHASA TV da Rediyo Muhammad Babandede OFR, OCM a Kano da yammacin ranar Asabar.
Sheikh Bala Lau ya ziyarci Muhammad Babandede ne domin yi masa ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa da Allah ya yi wa rasuwa da yammacin ranar Alhamis 26 Disamba, 2024 a ofishinsa da ke ginin gidan rediyo da talabijin na MUHASA.
Yayin ziyarar ta’aziyyar, Sheikh Bala Lau ya bayyana rashin Hajiya Hajara a matsayin babban rashi ga jama’a da dama.
Sheikh Bala Lau ya ce, suna tare da Muhammad Babandede a cikin yanayi na alhini da raɗaɗin rashin mahaifiyarsa.
Bayan ta’aziyyar rashin mahaifiyar Muhammad Babandede, Sheikh Bala Lau ya jinjina wa irin ƙoƙarin da ya yi wurin gina katafaren gidan rediyo da talabijin na MUHASA.
Mamallakin tashoshin MUHASA TV da Rediyo Muhammad Babandede OFR OCM, ya bayyana zuwan su Sheikh Bala Lau a matsayin nuna ƙauna gare shi da ahalinsa, ya kuma godiya da yadda aka ta yi wa mahaifiyarsa addu’a.
A tawagar ta Sheikh Bala Lau akwai Daraktan ‘Yan Agaji na ƙasa sheikh Mustapha Sitti da mataimakin shugaban alaramomin ƙungiyar Izala Sheikh Ahmad Sulaiman Kano da daraktan ayyuka Injiniya Ashiru Babandede da wasu manyan malamai da jami’an ƙungiyar na ƙasa.