Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jaddada muhimmanci aiwatar da taron ƙolin ƙasashen yankin tekun Guinea wato “Gulf of Guinea Commission” mai fafutukar kare yankin daga ayyukan masu fashin teku.
Shugaba Buhari ya ce zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da inganta tsaron yankin. Buhari na jawabin ne yayin wani taron kolin ƙasashen yankin tekun Guinea da aka gudanar an Accra babban birnin kasar Ghana ajiya Talata.
Shugaban ya kara da cewa tilas ne a ƙarfafa tarukan ƙungiyar ƙasashen yankin tekun Guinea da na shugabannin ƙasashen yankin domin samun damar tattauna matsaloli tare da lalubo hanyoyin magance su, domin samar da zaman lafiya, da tsaro da kuma ci gaban ƙasashen yankin tekun Guinea.
Shugaban ya tabbatarwa mambobin kungiyar kasashen cewa tarayyar Najeriya ta cimma nasarori da dama wajen yaƙar ayyukan masu fashin teku a yankin tekun Guinea, tare da bukatar da ƙasashen ƙungiyar da su samar da dokoki da za su haramta fashin teku, kamar yadda Najeriya ta yi.