Musa Gwadabe ya rasu ne a Kano yana da shekaru 86 a daren jiya Talata, bayan doguwar jinya, kamar yadda jaridar majiyarmu ta ruwaito.
A yanzu haka ake shirye shiryen gudanar da jana’izar marigayin da a gidansa da ke kan titin Maiduguri a Kano kamar yadda dan’ uwansa Nasiru Gwadabe ya bayyana.
Alhaji Musa Gwadabe wanda ya rike mukamin minista a lokacin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo na farko, daga shekarar 1999 zuwa 2003.
Ya kuma kasance sakataren gwamnatin jihar Kano a zamanin marigayi Sabo Bakin Zuwo, kuma ya kasance mamba a kwamitocin gudanarwa da dama.
Kafin rasuwarsa shi ne shugaban hukumar kula da harkokin horar da masana’antu, ITF.
Ya rasu ya bar ‘ya’ya 12 , da jikoki da kuma ‘yan uwa.
A wani bangaren kuma jami’ar Bayero da ke Kano ta sanar da rasuwar magatakardanta, Malam Jamil Ahmad salim, wanda ya rasu a safiyar yau Lahadi.
Tun da farko an wallafa sanarwar ne a hafin Facebook na jami’ar ta Bayero, inda aka sanarda al’ummar muslmi lokacin da za ai jana’izar marigayin.
Tuni dai aka yi jana’izar tasa a masallacin Juma’a da ke sabuwar Jama’ar dake kan titin zuwa Gwarzo a Kano.