Najeriya ta fara tattaunawa da ɓangarori da dama don duba yiwuwar shiga ƙungiyar kasashen G20 masu ci gaban tattalin arziki a duniya.
Shugaban Indiya Narendra Modi ne shugaban G20 a halin da ake ciki. Kazalika Afirka ta Kudu ce kadai mamba a cikin kungiyar daga Afirka.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bar Abuja a yau don halartar taron kasashen G20 a New Delhi, India, bisa gayyata ta musamman daga Firaiministan India, Narendra Modi.
Kamar yadda Mista Ngelale ya wallafa a shafukan sada zumunta, Shugaba Tinubu zai halarci wata tattaunawa a bayan fagen taron, wadda za a yi kan Najeria da Indiya da kuma taron kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Ya kara da cewa Shugaba Tinubu zai yi amfani da wannan dama wajen jan hankalin ƴan kasuwa da kamfanoni na ƙasashen duniya su ƙara zuba jari a Najeriya.