Zaɓabben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya musanta rahotannin da ke cewa ya gana da babban Jojin Najeriya a birnin London na ƙasar Ingila.
Wata sanarwa da ta samu sa hannun daraktan yaɗa labaru na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bayo Onanuga, ta bayyana labarin a matsayin ƙage maras tushe.
A cikin kwanakin nan ne wasu jaridu da kuma masu amfani da shafukan sada zumunta suka rinka yaɗa labarin yadda aka yi wata ganawar sirri, tsakanin Bola Ahmed Tinubu da babban Jojin Najeriya, Olukayode Ariwoola.
Labarin ya nuna cewa babban Sojin ya yi ɓadda-bami ta hanyar hawa keken guragu domin ganawa da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar a birnin London.
Sai dai sanarwar, wadda aka fitar ta ce an ƙirƙiri labarin ne domin sanya shakku a zukatan ƴan Najeriya game da nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaɓen da ya gabata.