• Home  
  • Shugaban Chadi Mahamat Deby zai yi wa wasu da aka ɗaure afuwa
- Kasashen Ketare

Shugaban Chadi Mahamat Deby zai yi wa wasu da aka ɗaure afuwa

Shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Deby, ya sanar da cewa zai yi wa wasu da aka ɗaure afuwa a matsayin wani mataki na samar da haɗin kai, yafiya da sulhu a ƙasar. Ya bayyana hakan ne yayin bikin cika shekaru 66 da samun ‘yancin kan Chadi, inda ya buƙaci ‘yan ƙasa su guje wa rarrabuwar kawuna […]

Shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Deby, ya sanar da cewa zai yi wa wasu da aka ɗaure afuwa a matsayin wani mataki na samar da haɗin kai, yafiya da sulhu a ƙasar.

Ya bayyana hakan ne yayin bikin cika shekaru 66 da samun ‘yancin kan Chadi, inda ya buƙaci ‘yan ƙasa su guje wa rarrabuwar kawuna tare da fifita muradun ƙasa.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kira a saki tsohon firaministan ƙasar kuma jagoran ƴan adawa, Succès Masra, wanda ke zaman hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari bayan an same shi da laifukan da suka haɗa da tayar da ƙiyayya da hannu a kisan kai, zarge-zargen da ya musanta.

Wasu ‘yan ƙasar na fatan cewa afuwar da shugaban zai yi za ta haɗa da Succès Masra da kuma wasu jagororin adawa takwas da aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekaru takwas bayan shirya zanga-zangar da gwamnati ta haramta.

Har yanzu shugaban bai bayyana sunayen waɗanda za su amfana da afuwar ba ko kuma ranar da za a sake su.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai