Firaministan Sifaniya ya buƙaci a haramta wa isra’ila shiga dukkanin gasar wasanni na duniya har sai ta daina abin da ya kira muguwar aika aikar da ta ke tafkawa.
Pedro Sanchez ya alaƙanta ta’asar da isra’ila ke yi a Gaza da wanda Rasha ke yi a Ukraine, inda ya ce ba abu bane da ya dace ba a bar ƙasashen biyu su riƙa shiga gasar wasanni.
Buƙatar haramta wa isra’ila shiga gasar wasanni, shi ne mataki na baya-bayan nan da gwamnatin Sifaniya ta bijiro da shi domin jan hankali kan abin da ta kira kisan ƙare dangin da ake yi a Gaza.
Tuni dai aka haramtawa Rasha shiga gasar wasannin duniya da dama.
Tun da farko ministan al’adu na Spaniya ya ce ƙasar sa za ta ƙauracewa gasar waƙa ta Eurovision ta 2026 idan har za a amince wa Isra’ila shiga gasar.

