Jirgin ruwan na kasar Denmark da ya iso gabar tekun Guinea daga birnin Amsterdam, ya ratsa kasashen Ghana, Togo, Najeriya, Kamaru da Congo, kafin ‘yan ta’addan su yi awon gaba da shi.
HedIkwatar rundunar sojin ruwan Najeriya, ta ce dakarunta sun kubutar da wani katafaren jirgin ruwa da ‘yan fashin teku suka sace a gabar tekun Guinea.
Kakakin mayakan ruwan sojojin na Najeriya, Commodore Ayo Olukayode Voughan, ya shaida wa MAJIYARMU cewa, ‘yan fashin teku sun afka wa jirgin dauke da manyan makamai a ruwan kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
Jirgin ruwan na kasar Denmark da ya iso gabar tekun Guinea daga birnin Amsterdam, ya ratsa kasashen Ghana, Togo, Najeriya, Kamaru da Congo, kafin ‘yan ta’addan su yi awon gaba da shi.
Daga bisani jirgin yakin sojojin Najeriya mai suna NNS Gongola tare da tallafin jirgin ruwan mayakan Faransa da ke wani aikin hadin gwiwa a yankin, ya sami nasarar kubutar da jirgin da Monjasha.
Ko da yake, ‘yan fashin tekun sun yi awon gaba da ma’aikatan jirgin ruwan guda shida
A halin yanzu, sojojin ruwan na Najeriya sun bazama neman mutane shida da ake garkuwa da su.