A wani ci gaban da aka samu bayan ziyarar da tawagar Malaman ta kai Jamhuriyar Nijar, sojojin da suka yi juyin mulkin sun ce a shirye suke su tattauna da Kungiyar ECOWAS.
Sabon Firaiministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan tawagar Malaman Najeriya ta tattauna da shugaban mulkin sojan kasar, Janar Abdourahmane Tchiani ranar Asabar a birnin Yamai.
Wannan ne karon farko da sojojin suka nuna alamar yin sulhu tun bayan da suka kifar da gwamnatin Mohammed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.
Firaiministan ya ce yana fata nan da ‘yan kwanaki kadan masu zuwa, za su fara tattaunawa da ECOWAS, sannan kuma ya bayyana cewa takunkuman da ECOWAS ta ƙaƙaba wa kasar Nijar, wadanda suka jefa ta cikin mawuyacin hali, rashin adalci ne.
Ali Mahamane Lamine Zeine ya kara da cewa takunkuman sun saba wa dokokin kungiyar ta ECOWAS, ya kuma kara da cewa ba za su amince a gindaya musu wani sharadi kafin a cire takunkuman ba.