SojojiSun Kashe Yan Bindiga 13 Tare Da Ceto Yan kasuwa A Sakoto

Sojoji sun kashe wasu da ake zargin ’yan bindiga ne da suke ƙoƙarin yi garkuwa da ayarin ’yan kasuwa a kan hanyar Tarah–Karawa da ke Sabon Birni a Jihar Sakkwato.

’Yan kasuwar na kan hanyarsu daga ƙauyen Tarah zuwa kasuwar mako a Sabon Birni ne lokacin da ’yan bindiga suka kai musu hari a Kwanan Akimbo da misalin karfe 8 na safe.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa sojojin da ke sansani a Kurawa sun ji karar harbe-harbe, suka garzaya wajen, inda aka yi musayar wuta na kusan sa’a guda.

“Sojoji sun yi musu luguden wuta, daga baya ’yan bindigar suka ja da baya suka tsere zuwa maɓoyarsu a can bayan rafin.

“Mun ƙirga gawarwakin ’yan bindiga tara a yankinmu, sannan aka gano wasu hudu a dajin kusa da rafin. Sojoji kuma sun kwashe makamai da babura da dama suka kai Kurawa,” in ji wani mazaunin.

Ya ƙara da cewa mutane biyu ne suka samu raunuka, suna karbar magani a asibiti, amma dukkan ’yan kasuwar sun tsira ba tare da wani rauni ba. “Babu asarar rayuka a ɓangaren sojoji,” in ji shi.

Al’ummomin Kurawa da maƙwabtansu sun yi murna da nasarar da sojojin suka samu.

Ɗan majalisar dokokin jihar da ke wakiltar Sabon Birni, Hon. Aminu Boza, ya ce an gano gawarwakin aƙalla tara daga cikin ’yan bindigar, kuma bincike na ci gaba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *