Labarai
Dillallan Ƙwaya Sun Shiga Komar NDLEA A Faɗin Ƙasar Nan
A taronta na manema labarai na wannan makon Hukumar yaƙi da sha da safarar miyagun ƙwayoyi, NDLEA, ta ce jami’anta sun kama lodin tabar wiwi nau’in skunk a ɓoye a cikin gwangwanayen tumatir da wasu ƙwayoyin kuma da aka cusa a cikin tsofaffin tufafi da niyyar kai wa Dubai.

