Mutanen da suka mutu a haɗarin kwale-kwale a Sokoto sun kai 48
Kimanin mutum 48 ne suka mutu yayin da ake ci gaba da neman yara 12 bayan haɗarin jirgin ruwa da ya faru a yankin Goronya da ke jihar Sokoto. Akasarin waɗanda lamarin ya rutsa da su yara ne waɗanda ke kan hanyar zuwa gona a safiyar jiya Alhamis. A tattaunawarsa da BBC, ɗan majalisar tarayya […]

