Shin da gaske gwamnati za ta fara cire ₦7,500 a kowace ₦100,000 da aka tura?
Gwamnatin Tarayya ta umarci bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi da su fara cire harajin VAT na kaso 7.5 cikin 100 a kan cajin da ake dauka na kowacce hada-hadar kudin da suka kai 100,000. Umarnin, wanda Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (NRS) ta bayar, zai fara aiki ne daga ranar Litinin, 19 ga watan […]