Gwamnatin Tarayya ta umarci bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi da su fara cire harajin VAT na kaso 7.5 cikin 100 a kan cajin da ake dauka na kowacce hada-hadar kudin da suka kai 100,000.
Abin da ya sauya
Sabuwar dokar ba ta kawo harajin VAT kan ainihin kuɗin da ake tura wa kai tsaye ba. Harajin zai shafi kuɗin da bankuna ko cibiyoyin hada-hadar kasuwanci ke cajin ku idan ka yi amfani da tsarin tura kudi.
Misali, idan banki ya caje ku ₦100 don tura kuɗi, VAT zai kasance ₦7.50 ne kan wannan kuɗin cajin, ba kan ainihin ₦100,000 da kake tura wa ba.
- Kwankwaso ya karyata rahotan Premium Times na cewa ya goyi bayan gwamnan Kano zuwa APC
- Kwankwaso ya karyata rahotan Premium Times na cewa ya goyi bayan gwamnan Kano zuwa APC
Waɗanne abubuwa dokar za ta shafa?
Sanarwar da aka aika wa kwastomomi ta bayyana cewa sabon harajin na VAT zai shafi:
Me ya sa gwamnati ke yin haka?
Jami’ai sun ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin daidaita tattarawa da biyan harajin VAT a dukkan ayyukan kuɗi na lantarki da kuma ƙara samun kuɗaɗen shiga ga gwamnati a cikin tattalin arzikin zamani da ke bunƙasa a Najeriya.
Duk da cewa VAT kan mu’amalar banki ba sabon abu ba ne, NRS yanzu tana tilasta bin ƙa’ida ɗaya a dukkan hanyoyi.
Shin wannan ƙarin haraji ne?
Kamfanonin biyan kuɗi kamar Moniepoint sun bayyana cewa wannan ba sabon caji ba ne daga bankuna ko cibiyoyin hada-hadar kudi, illa kawai wajibi ne na doka. Za a nuna VAT a fili a takardun mu’amala da bayanan asusu domin kwastomomi su ga abin da aka caje su.
Yaya yake da sauran harajin bankuna?
A watan Disamba, bankuna sun fara cire ₦50 a matsayin harajin stamp duty kan dukkan ₦10,000 zuwa sama da aka tura, bisa sabuwar dokar haraji. Wannan caji, wanda a da ake kira EMTL, yanzu an sake masa suna stamp duty, kuma ana cajinsa sau ɗaya ne kawai kan mu’amalolin da suka cancanta.
Abin da ya kamata kwastomomi su sani
Daga ranar 19 ga Janairu, za ku ga ƙarin kashi 7.5 cikin ɗari na VAT a kan kuɗin cajin da kuka saba biya tura kuɗi, mu’amalar USSD da fitar da kudi ta katin ATM.
Kuɗin zai tafi kai tsaye ga gwamnati, ba bankuna ba.
AMINIYA