Harajin Trump Ba Zai Sa Mu Mika Wuya Ba – China

China ta dage cewa ba za ta mika wuya ba, duk da matsin da take fuskanta daga shugaba Trump na lafta mata haraji, amma ta ce idan an nemi ayi sulhu a shirye take.

Ma’aikatar kasuwancin kasar ta ce kofar tattaunawa a buɗe take.

Rahotanni sun ce dama sun jima cikin shiri, sannin cewa irin wannan yanayi zai taso, kuma suna ganin Amurka ita tafi bukatar China.

Akwai rahotanni da ke cewa manyan masana tattalin arziki a jam’iyyar kasar ta kwaminisanci na tattauna hanyoyin taimakawa ‘yan kasar a wannan gaba da ake ciki na yakin kasuwanci.

Amurka ta lafta harajin kashi 125 kan kayayyakin China.

Yayin da ita kuma China ta mayar da martani da harajin kashi 84 kan kayayyakin Amurka.

Post masu alaƙa

DSS ta kama waɗanda ake zargi da sace Farfesa A Nasarawa

An gurfanar da waɗanda ake zargi da sace ɗaliban Oyo

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kwace kadarorin Godwin Emefiele