Babban Labari
Dubun masu ƙera muggan makamai a Filato ta cika
Dubun wasu masu ƙera muggan makamai ta cika a yankin Lantang da ke Jihar Filato mai yawan fama da rikice-rikice da hare-hare. Sojojin Rundunar Operation Enduring Peace sun kama manyan bindigogi uku, ƙirar AK-47 guda biyu da kuma ƙirar G3 guda ɗaya a hannun masu ƙera makamai ba bisa ka’ida ba. Mutanen sun shiga hannun […]

