Kwamishinan Yan sandan Kano Ibrahim Bakori Ya Ce Sun Fara Bincike Don Gano Abinda Ya Halaka Kwamandan Yaki Da Kwacen Waya.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce tuni ya bayar da Umarnin gudanar da cikakken bincike, kan abinda ya yi sanadiyar mutuwar Kwamandan yaki da fadan daba da kwacen waya, Inuwa Salisu Sharada. CP Bakori ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da Wakilin mu, Mujahid Wada, a shelkwatar rundunar dake […]