Kwamishinan Yan sandan Kano Ibrahim Bakori Ya Ce Sun Fara Bincike Don Gano Abinda Ya Halaka Kwamandan Yaki Da Kwacen Waya.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce tuni ya bayar da Umarnin gudanar da cikakken bincike, kan abinda ya yi sanadiyar mutuwar Kwamandan yaki da fadan daba da kwacen waya, Inuwa Salisu Sharada.

CP Bakori ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da Wakilin mu, Mujahid Wada, a shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai Kano, a ranar Alhamis.

Kwamishinan yan sandan ya Kara da cewa duk abunda bincike ya gano za su bayyana wa al’umma gaskiyar, ammm jama’a su kwantar da hankali.

A ranar Larabar data gabata Kwamandan ya rasa ransa bayan zuwan wasu jami’an tsaro da suka shiga gidansa da yan uwansa suka ce Kama shi za su yi.

Tuni dai Yan uwan marigayin da abokan aikinsa suka roki Gwamnatin ta tabbata an hukunci wadanda aka samu da Aikata laifin.

Gwamnan Alhaji Abba Kabir, ya ce lokacin da ya samu labarin rasuwarsa kwamandan, kasa yin bacci don haka wajibi ne a hukunta dukkan wanda yake da hannun kan lamarin

Post masu alaƙa

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Yan Sandan a Kano sun kama mutane 244, ciki har da 117 da ake zargi da fadan daba.

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.