• Home  
  • Tinubu Ya Amince Da Bayar Da Lasisin Ci Gaba Da Aikin Haƙar Mai Na Kolmani
- Babban Labari - Labarai

Tinubu Ya Amince Da Bayar Da Lasisin Ci Gaba Da Aikin Haƙar Mai Na Kolmani

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da ci gaba da aikin haƙar man fetur na Kolmani da ke tsakanin jahohin Bauchi da Gombe. Ministan albarkatun mai na Najeriya, Heineken Lokpobiri ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Nneamaka Okafo ya fitar ranar Lahadi . Ministan ya ce, […]

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da ci gaba da aikin haƙar man fetur na Kolmani da ke tsakanin jahohin Bauchi da Gombe.

Ministan albarkatun mai na Najeriya, Heineken Lokpobiri ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Nneamaka Okafo ya fitar ranar Lahadi .

Ministan ya ce, “Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da tabbatar an bayar da duka lasisin da suka rage domin samun damar ci gaba da aikin na Kolmani”.

Ya ce tunin gwamnatin Najeriyar ta samar da wata cibiyar nazarin albarkaun man fetur da iskar gas a ƙaramar hukumar Alƙaleri da ke jihar Bachi domin tabbaar da an samu nasarar ɗorewar ci gaba da aikin.

A watan Nuwamban 2022 ne aka fara aikin shirin haƙar mai na Kolmani, wanda ya bayar da damar soma neman ɗanyen man a shiyar arewacin Najeriya, wanda yanki ne na kogin Kolmani mai tarin arzikin man da ke tsakanin jahohin na Bauchi da Gombe.

A makon da ya gabata shugaban kamfanin haƙar man fetur na ƙasa, Bayo Ojulari ya shaida wa BBC cewa kamfanin NNPCL ɗin zai ci gaba da aikin tono man a rijiyar ta Kolmani.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai