Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da ta gaggauta komawa kotu domin neman a soke umarnin da ya ba ta damar rufe asusun gwamnatin Jihar Osun.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, shugaban ya bayyana rashin jin daɗinsa kan matakin da hukumar ta ɗauka, yana mai cewa ba lokacin da ya dace aka aiwatar da shi ba, musamman yayin da jihar ke dab da gudanar da zaɓen gwamna.
“Dole ne in bayyana cewa abin ya ba ni kunya ƙwarai. Ba wai saboda EFCC ta aiwatar da aikinta bisa umarnin kotu ba ne, sai dai saboda lokacin da ta ɗauki wannan mataki,” in ji Tinubu.
Ya ƙara da cewa duk wani mataki da hukumomin gwamnatin tarayya suka ɗauka, jama’a kan danganta shi da shugaban ƙasa, ko da kuwa bai da masaniya a kansa.
Tinubu ya jaddada cewa tun bayan hawansa mulki ya kauce wa tsoma baki cikin ayyukan EFCC da sauran hukumomin bincike domin su gudanar da aikinsu cikin ’yanci da ƙwarewa.
“Na kasance ina jaddada cewa dole ne a bar hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran hukumomin tabbatar da doka su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa, ba tare da tsoro, son rai ko katsalandan na siyasa ba,” in ji shi.
Sai dai shugaban ya ce, duk da cewa har yanzu bai samu cikakken bayani kan dalilan da suka sa EFCC ta nemi umarnin kotu na rufe asusun gwamnatin Osun ba, yana ganin lokacin da aka ɗauki matakin bai dace ba.
Ya ce kasancewar Jihar Osun na shirin gudanar da zaɓen gwamna, ya zama wajibi a guji duk wani mataki da zai iya haifar da zargin cewa ana amfani da hukumomin Gwamnatin Tarayya wajen yin katsalandan a harkokin zaɓe.
“Saboda haka, na umarci EFCC da ta gaggauta komawa kotu domin neman a soke wannan umarni, tare da dakatar da duk wani matakin da ta ɗauka kan gwamnatin Jihar Osun dangane da wannan lamari,” in ji shugaban.
EFCC ta samu umarnin kotu a ranar 5 ga Agustan 2026 na rufe asusun gwamnatin Jihar Osun.
Sai dai zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, hukumar ba ta fitar da ƙarin bayani kan dalilan da suka sa ta nemi umarnin kotun ba.
