Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce za ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da aiyukan daba da fataucin miyagun ƙwayoyi, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin da ke da alhakin yaƙi da waɗannan laifuka.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar bayan ziyarar aiki da shugaban kwamitin haɗin gwiwa na Jihar Kano kan yaƙi da miyagun kwayoyi , Barrista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya kai hedikwatar rundunar da ke Bompai.
A cewar shugaban kwamitin, manufar ziyarar ita ce gabatar da shugabannin kwamitin ga rundunar da bayyana aiyukan da aka ɗora musu da kuma neman haɗin gwiwa wajen yaƙi da shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.
Ya ce kwamitin zai ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro ta hanyar wayar da kan jama’a da kuma haɗa kai da al’umma da tattara bayanan sirri domin daƙile ayiyukan masu safara da dillalan miyagun ƙwayoyi.
Anasa jawabin kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce rundunar a shirye take kuma zata yi aiki tare da kwamitin wajen yaƙi da daba da fataucin miyagun ƙwayoyi.
Ya ce yaƙi da shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi ba zai yi tasiri ba sai idan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa kai wajen gudanar da ayyukansu da musayar bayanan sirri da sauran matakan tsaro.
A cewarsa, hukumomin tsaro sun gano cewa shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa ayyukan daba, musamman a cikin birnin Kano.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga iyaye, sarakunan gargajiya, malamai da shugabannin al’umma su riƙa bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka.
Rundunar ta ce duk wanda aka samu da laifin fataucin miyagun kwayoyi za a kama shi sannan a gudanar da bincike kafin a gurfanar dashi a gaban kotun domin ya fuskanci hukunci.





