• Home  
  • Tinubu ya isa Kenya don halartar taron ƙoli na Afirka da Faransa
- Babban Labari

Tinubu ya isa Kenya don halartar taron ƙoli na Afirka da Faransa

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya isa Nairobi, babban birnin Kenya gabanin taron ƙoli na Afirka da Faransa da za a shafe yini biyu ana yi. Shugaba Tinubu ya samu tarba daga jami’i a gwamnatin Kenya, Musalia Mudavadi wanda kuma shi ne sakataren da ke kula da harkokin da suka shafi ƙasashen ƙetare. Akwai kuma […]

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya isa Nairobi, babban birnin Kenya gabanin taron ƙoli na Afirka da Faransa da za a shafe yini biyu ana yi.

Shugaba Tinubu ya samu tarba daga jami’i a gwamnatin Kenya, Musalia Mudavadi wanda kuma shi ne sakataren da ke kula da harkokin da suka shafi ƙasashen ƙetare.

Akwai kuma Ministar harkokin waje ta Najeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu da Jakadan Kenya a Najeriya, Amb. Isaac Parashina.

Taron zai ƙara ƙarfafa ƙudirin Najeriya na zurfafa alaƙa da kuma haɗin kai da sauran ƙasashen Afirka da kuma Faransa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000