Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Dokta Bernard Mohammed Doro daga Jihar Filato a matsayin sabon Minista a gwamnatinsa.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da fitar a wannan Talatar, inda ya ce naɗin zai tabbata ne bayan amincewar Majalisar Dattawa.
- Gwamnatin Tarayya Ta Ce EFCC Ta Kwato Sama Da Naira Biliyan 500 A Shekara 2
- Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutanen Da Suka Kashe Ma’aikacin Jami’a A Kano
Naɗin Dokta Doro na zuwa ne bayan zaben Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda da aka yi a matsayin Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa a watan Yuli, wanda a baya yake riƙe da muƙamin Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci.
Kazalika, sanarwar ta ce tuni an miƙa wa Majalisar Dattawa sunan sabon ministan domin tantancewa.