Kungiyar Matasa masu rajin ci gaban Arewacin NIjeriya, Northern Youth Patriotic Group, ta ce akwai son rai da son zuciya a hukuncin kotun sauraron ƙarrakin zaben gwamnan jihar Kano da aka yi a ranar Laraba.
Shugaban kungiyar Injiniya Aminu Adam Takai ne ya bayyana hakan, a wani taron manema labarai da ya gudana a Kano.
Aminu Adam Takai ya ce akwai bukatar a yi duba na tsanaki kan yadda hukuncin ya gudana, domin akwai rashin adalci a cikinsa matuka.
”Abun da akai na soke kuri’u dubu dari da sittin da biyar da dari shida sittin da biyar 165, 663 na kuri’un gwamnan jahar Engr. Abba Kabir Yusuf na jam’iyar NNPP tsantsar rashin adalci ne kuma da rashin son gaskiya”.
”Idan kuwa har za’a soke wadannan kuri’u to kamata ya yi a ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba, bisa cewa kuri’un da aka soke sun fi tazarar abin da aka ce an ci zaben da su ”.
Ya ce bai kamata wasu cikin al’umma su yi murnar wannan nasara ba, saboda hakan ya nuna cewa ba su san yadda dokar zabe ta ke ba, kuma hakan ya nuna sun nuna goyon bayan rashin adalci ne.
Injiniya Aminu Adam Takai ya kuma bukaci banagaren shari’a a Nijeriya, da ya dauki matakin da ya dace domin bai wa mai gaskiya abarsa.