• Home  
  • Tinubu ya tsawaita wa’adin shugaban hukumar kwastam na tsawon watanni shida
- Babban Labari

Tinubu ya tsawaita wa’adin shugaban hukumar kwastam na tsawon watanni shida

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya amince da ƙarin wa’adin watanni shida ga Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), Adewale Adeniyi. Sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma’a ta ce wa’adin Adeniyi na yanzu zai ƙare ne a ranar 1 ga watan Agustan 2026. Sai […]

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya amince da ƙarin wa’adin watanni shida ga Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), Adewale Adeniyi.
Sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma’a ta ce wa’adin Adeniyi na yanzu zai ƙare ne a ranar 1 ga watan Agustan 2026.
Sai dai shugaban ƙasar ya amince da ƙarin wa’adin watanni shida, wanda zai ƙare a watan Fabrairun 2027.
Fadar shugaban ƙasa ta ce an ba Adeniyi wannan ƙarin wa’adi ne domin ya kammala aiwatar da shirin National Single Window tare da tabbatar da sauyin shugabanci cikin tsari a cikin hukumar.
A lokacin ƙarin wa’adin, Adeniyi zai yi aiki tare da kwamitin Hukumar Kwastam domin tabbatar da karin girma ga jami’an da suka cancanta zuwa mukamin Kwanturola, tare da ritayar dole ga jami’an da suka kai shekaru 60 ko kuma suka yi shekara 35 a aikin gwamnati.
Adeniyi ya shiga aikin Kwastam bayan ya kammala karatu a Jami’ar Obafemi Awolowo a ƙarshen shekarun 1980. Ya riƙa hawa mukamai a hukumar inda ya zama Mataimakin Kwanturola a 2012, Kwanturola a 2017, Mataimakin Shugaban Hukumar Kwastam a 2020, sannan ya zama mukaddashin Mataimakin Shugaban Hukumar a Janairun 2023.
Shugaba Tinubu ya naɗa shi a matsayin Shugaban Hukumar Kwastam a watan Yunin 2023. Ana sa ran ƙarin wa’adin zai taimaka wajen ci gaba da sauye-sauye da gyare-gyare da ake aiwatarwa a hukumar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000