• Home  
  • Tinubu zai karɓo sabon bashin fiye da dala biliyan 20
- Labarai

Tinubu zai karɓo sabon bashin fiye da dala biliyan 20

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta sahale masa shirin karɓo sabon bashin dala biliyan 20.51 da kuma yuro biliyan 1.45 domin gudanar da muhimman ayyukan raya ƙasa a shekarun 2026 zuwa 2027. Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasiƙar Tinubu a yayin zaman majalisar na ranar Talata. A cewar wasiƙar, […]

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta sahale masa shirin karɓo sabon bashin dala biliyan 20.51 da kuma yuro biliyan 1.45 domin gudanar da muhimman ayyukan raya ƙasa a shekarun 2026 zuwa 2027.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasiƙar Tinubu a yayin zaman majalisar na ranar Talata.

A cewar wasiƙar, za a yi amfani da kuɗaɗen wajen bunƙasa kayayyakin more rayuwa da kuma cike giɓin kuɗaɗen da ake buƙata a muhimman fannoni da suka haɗa da wutar lantarki, sufuri, kiwon lafiya, ilimi, noma, samar da ruwa, tsaro da ayyukan yi.

Tinubu ya ce ya miƙa buƙatar ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa domin samun amincewarta cikin gaggawa, ta yadda za a fara aiwatar da ayyukan da aka tsara.

Ya ƙara da cewa, ayyukan da aka aiwatar da kuɗaɗen za su tabbatar da  rage talauci, bunƙasa ƙwarewa da sana’o’i, tare da ƙarfafa samar da abinci a ƙasar.

Bayan karanta wasiƙar, Akpabio ya miƙa buƙatar ga Kwamitin Majalisar Dattawa kan Basussukan Cikin Gida da na Ƙasashen Waje, ƙarƙashin jagorancin Sanata Haruna Manu, domin nazari.

Aminiya ta ruwaito cewa, wannan sabuwar buƙatar neman bashi na zuwa ne bayan kimanin watanni biyar da Majalisar Tarayya ta amince da bashin dala miliyan 516.3, domin gudanar da aikin gina babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry, ɗaya daga cikin manyan ayyukan more rayuwa na gwamnatin Tinubu a ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai