• Home  
  • Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya Galadima ya rasu
- Babban Labari - Wasanni

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya Galadima ya rasu

Tsohon shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya NFF Ibrahim Galadima ya rasu yana da shekara 74. Marigayin ya rasu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya a yau Asabar. Za a yi jana’izar Ibrahim Galadima ne a Masallacin Juma’a na waje da ke Fagge a gobe Lahadi da misalin ƙarfe 10 na safe. Galadima wanda […]

Tsohon shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya NFF Ibrahim Galadima ya rasu yana da shekara 74.

Marigayin ya rasu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya a yau Asabar.

Za a yi jana’izar Ibrahim Galadima ne a Masallacin Juma’a na waje da ke Fagge a gobe Lahadi da misalin ƙarfe 10 na safe.

Galadima wanda ya jagoranci NFF tsakanin 2002 zuwa 2006, ya rasu ya bar mata ɗaya ba tare da ko ɗa guda ba.

An dai haife shi a ranar 14 ga watan Yunin 1951, kuma ana masa kallon masu ruwa da tsakin da suka kafa ƙungiyar kwallon ƙafa ta Kano Pillar a 1991.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai