• Home  
  • Ƴan bindiga sun sace basarake da matarsa a jihar Kwara
- Babban Labari

Ƴan bindiga sun sace basarake da matarsa a jihar Kwara

Wasu da ake zargin yan bindiga sun kai farmaki fadar wani basarake, tare da sace shi da matarsa a ƙauyen Olayinka, da ke ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara. Rahoton ya nuna cewa maharan sun kai farmaki fadar Oba Salman Aweda da misalin ƙarfe 1:40 na dare ranar Asabar, inda suka rika harbi sama domin […]

Wasu da ake zargin yan bindiga sun kai farmaki fadar wani basarake, tare da sace shi da matarsa a ƙauyen Olayinka, da ke ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara.

Rahoton ya nuna cewa maharan sun kai farmaki fadar Oba Salman Aweda da misalin ƙarfe 1:40 na dare ranar Asabar, inda suka rika harbi sama domin tsoratar da mazauna yankin kafin su tafi da basaraken da matarsa da kuma mutum daya

Rahotanni na cewa kawo yanzu ba a san inda akai basaraken da sauran mutanen ba, amma hukumomin tsaro na ci gaba da gudanar da bincike kan lamari.

Karin bayani na tafe.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000