Tsohon shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya bar mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina inda ya tare tun bayan saukarsa daga mulki.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da tsohon maitaimaka masa akan harkokin ƴaɗa labarai Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Sai dai malam Garba shehu bai bayyana inda tsohon shugban ya komada zama ba.
Malam Garba Shehu ya ce, dattijon baya samun yadda yake so a garin na Daura, duk da ya bar kan mulki, mutane su na yawan kai masa ziyara, saboda haka ya sake lulawa zuwa wani wuri mai nisa domin ya yi rayuwa cikin sukuni.
Ya ce, Buhari ya koka da irin cinci-rindon da masu ziyara suke yi masa dare da rana a lokacin da yake kokarin samun hutu.
A cikin jawabin nasa malam Garba Shehu ya ce, dama Buhari ya tafi Daura ne da nufin ya samu irin rayuwar da yake so ta rashin hayaniya, amma sai ya fahimci ba haka lamarin yake ba.