Shugaban kasar Türkiya, Recep Tayyip Erdogan ya yi buɗe bakin farko na wannan shekarar a birnin kwantena na Karacasu tare da mutanen da suka gamu da ibtila’in girgizar kasar da ta afku a ranar 6 ga watan Fabrairu ta shafa.
A cikin jawabin da ya gabatar, Erdogan ya bayyana cewa Ramadan na bana ya zo ne a daidai lokacin da aka samu asarar rayuka sakamakon girgizar kasar.
Ya kuma yi fatan Allah ya ji kan ‘yan kasar da suka rasa rayukansu a girgizar kasar tere da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalansu da kuma fatan samun lafiya cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata da ake ci gaba da kula da.
Shugaba Erdogan ya kuma bayyana cewa babu wanda ke da tantama game da munin bala’in da ya shafi rayukan ‘yan kasar miliyan goma sha huɗu.
A cewarsa, wajibi ne kuma alhakinsu ne a matsayin ‘yan uwa wadanda girgizar kasar ta shafa da su san cewa ba za su yi watsi da su ba. Erdogan ya kuma tabo batun yaki da ta’addanci a cikin jawabin nasa, inda ya bayyana cewa za su cigaba da ɗaukar matakin da ya dace wajen magance ‘yan ta’adda da ke barazana ga kasar da kuma mai da hankali wajen karya munanan tsare-tsare na masu goyon bayan wadannan ‘yan ta’addan da masu ba su makamai da alburusai.