• Home  
  • Ukraine ta gano gawarwakin ƴan Najeriya da aka kashe cikin sojojin Rasha
- Babban Labari - Labarai

Ukraine ta gano gawarwakin ƴan Najeriya da aka kashe cikin sojojin Rasha

Hukumar leƙen asirin Ukraine, UDI ta bayyana cewa ta gano wasu ƴan Najeriya biyu da aka kashe a matsayin sojojin hayar Rasha a yayin farmakin da suka kai yankin Luhansk. Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya tare da hotunan mutanen, inda ta nuna su kafin mutuwarsu da kuma […]

Hukumar leƙen asirin Ukraine, UDI ta bayyana cewa ta gano wasu ƴan Najeriya biyu da aka kashe a matsayin sojojin hayar Rasha a yayin farmakin da suka kai yankin Luhansk.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya tare da hotunan mutanen, inda ta nuna su kafin mutuwarsu da kuma wani hoto da ya shafi iyalan ɗaya daga cikinsu.

Wannan na zuwa ne makonni biyu bayan samun labarin rasuwar wani matashi a Kano wanda ake zargin ya shiga aikin sojin haya na ƙasar Rasha.

Bayanan da jami’an leƙen asirin sojin Ukraine a yankin Luhansk suka fitar sun bayyana sunayen mutanen da Hamzat Kazeen Kolawole da kuma Mbah Stephen Udoka.

Sanarwar ta ƙara da cewa mutanen biyu sun yi aiki a bataliyar sojin Rasha ta 423 mai kula da tankokin yaƙi.

Rahotanni na cewa ba su kaɗai ba ne suka shiga aikin soja a Rasha, domin akwai ƴan Najeriya da dama, ciki har da wasu daga Kano.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai