• Home  
  • Wani Mutum Ya Zuba Shinkafar Bera A Abincin Da Ya Ci A Kano
- Babban Labari - Labarai

Wani Mutum Ya Zuba Shinkafar Bera A Abincin Da Ya Ci A Kano

Wani mutum ya zubawa abincinsa shinkafar Bera, akan Titin Audu Bako Way Dake Jihar Kano. Ana Zargin mutumin ya zuba gubar ce bayan ya sayi Wata shinkafa da miya kuma Sai da ya fara ci sannan ya nunawa mutane abunda ya zuba cikin abincin. Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa, ya shiga gidan […]

Wani mutum ya zubawa abincinsa shinkafar Bera, akan Titin Audu Bako Way Dake Jihar Kano.

Ana Zargin mutumin ya zuba gubar ce bayan ya sayi Wata shinkafa da miya kuma Sai da ya fara ci sannan ya nunawa mutane abunda ya zuba cikin abincin.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa, ya shiga gidan abinci ne ya siyo sannan ya zuba gubar kafin ya ci.

Yanzu haka an garzaya da shi zuwa Asbitin Nassarawa don bashi kulawar gaggawa sakamakon faduwa da ya yi kuma baya cikin haiyacinsa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai