Yanzu wata 11 ke nan bayan kisan gillar da aka yi wa tawagar mafarautan Jihar Kano a Jihar Edo, a mma har yanzu gwamnatin jihar ba ta cika alƙawarinta na biyan diyya ga iyalansu ba.
Mafarauta 16 daga Jihar Kano be aka yi wa kisan gilla a yayin da suke hanyarsu ta komawa Kano daga Jihar Ribas, ranar 28 ga Maris, 2025.
’Yan banga ne suka tare motar mafarautan tare da far musu a yankin Uromi da ke Jihar Edo, bisa zargin cewa ’yan fashi ne, duk kuwa da cewa mafarautan sun gabatar musu da shaidar kasancewarsu mafarauta.
Maharan sun yi musu dukan kawo wuƙa tare da ƙone gawarwakinsu, lamarin da ya tayar da hankula tare da kiraye-kirayen ɗaukar mataki.
Gwamnatin Jihar Edo ta yi alƙawarin biyan diyya da tallafi ga iyalan mafarautan. Ta kuma sanar da cewa ta kama wasu mutane da zargi da hannu a kisan mafarautan, waɗanda ’yan asalin kauyen Torankawa ne a Ƙaramar Hukumar Bunkure ta Jihar Kano.
Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya ziyarci kauyen Torankawa tare da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ya yi alƙawarin ba da diyya ga iyalan da abin ya shafa da kuma tabbatar da cewa an hukunta waɗanda suka aikata laifin.
- Bukatunmu kan gyaran dokar zaɓen Najeriya – El-Rufai
- Saudiyya za ta zuba jarin biliyoyin Dala a Siriya
Halin da iyalansu ke ciki
Sai dai kusan shekara guda bayan wannan alkawari, iyalan sun ce ba su samu wani tallafi ko diyyar da gwamnati ta yi musu alƙawari ba.
Sun bayyana cewa jinkirin ya ƙara musu raɗaɗin rashi tare da haifar da tambayoyi kan gaskiya da adalci.
Ibrahim Isa, wanda shi kaɗai ya tsira a harin, ya ce rayuwarsa ta rikide zuwa wahala tun bayan dawowarsa. Ya bayyana cewa duk da alƙawarin tallafi daga hukumomin Kano, har yanzu ba a cika musu ba.
Hauwa’u Isa, matar daya daga cikin waɗanda aka kashe, ta roki gwamnatin Kano ta tallafa mata da ’ya’yanta uku. “Sun yi alƙawarin diyya da adalci ga mijinmu. Ina fatan ba za a bar wannan magana ta zama siyasa kawai ba,” in ji ta.
Malam Bala Dutse, wanda aka kashe ɗansa a lamarin, ya jaddada cewa ba za a bar batun ya shuɗe ba tare da an yi adalci ba.
Ya ce: “Tun lokacin da aka kashe ’ya’yanmu, gwamnati ta ce ta kama wasu, amma har yanzu ba mu samu sahihin bayani kan shari’ar ba.”
Zahura Haruna, wadda sabuwar amarya ce a lokacin da aka kashe mijinta a harin, ta ce rayuwarta ta koma wahala bayan aure mai tsawon kwanaki 40 kacal da mijinta da aka kashe.
Cikin hawaye ta ce, “Na zama nauyi ga iyalan mijina. Yanzu muna dogaro da maƙwabta wajen samun abinci.”
Mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce: “Gwamnatin Kano ba za ta bar wannan batu ya shuɗe haka kawai ba. Mun yi duk abin da ya kamata, muna jiran su ne kawai.”
A nata ɓangaren, Kwamishinan Bayani da Tsare-tsare na Edo, Kassim Afegbua, ya ce Gwamna Okpebholo ya nuna jagoranci mai kyau tun bayan faruwar lamarin.
Ya kara da cewa: “Na tuna ya yi alkawarin diyya, kuma ina da tabbacin cewa ya cika. Idan akwai sabanin haka, zan sanar da ku daga baya
