Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 288 da ake zargin ’yan daba ne a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihar.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama mutanen da makamai masu hatsari, ciki har da bindigogi ƙirar gida, wuƙaƙe da adduna.
Ya bayyana cewa an yi wannan kamen ne domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da zaɓen.
- Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12 Tare Da Jikkata 5 A Kano
- Masu Ruwa Da Tsaki A Unguwar Sharada Sun Amince Da Dokoki 29 Don Gyara Tarbiya.
Ya ce suna ci gaba da bincike, kuma duk wanda aka tabbatar na da laifi za a gurfanar da shi a kotu.
Kiyawa, ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da tabbatar da doka da oda.
A gefe guda kuma, ya yi gargaɗin cewa rundunar ba za ra lamunci tashin hankali ko rikicin siyasa a Kano ba.



