Home » Yadda kyautar Ballon d’Or ta bar baya da kura a birnin Paris

Yadda kyautar Ballon d’Or ta bar baya da kura a birnin Paris

by Suraj Na iya Kududdufawa
0 comment

Kyatar nan ta Ballon d’Or da aka bayar a birnin Paris na kasar Faransa ta bar baya da kura inda ake ganin kamar akwai son zuciya da kin gaskiya.

Ita dai wannan kyauta ana bayar da ita ne ga dukkanin danwasan da yafi kokari idan aka yi duba da wasu alkaluma aka dora su a mizani a kwallon kafa.

A kakar wasan da ta gabata ana gamin cewa dan wasan Real Madrid dan asalin kasar Brazil wato Viniciuos shine ya cancanta amma amma kwatsam sai alkaluma suka sauya aka baiwa danwasan Manchester City wato Rodri.

Tun kafin lokacin bayar da kyautar mahukuntan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid suka samu labarin siyasa ta shigo ciki kan cewar hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai Uefa ta shiga ta fita ancire sunan danwasan Real Madrid daga matsayi na daya sakamakon takun sakar dake tsakaninsu da Real Madrid.

Daga jin haka mahukuntan na Madrid suka fasa zuwa wajen bikin wanda dukkanin wasu abubuwa da Real Madrid ta lashe kama daga gwarzon mai horas wa da kungiya mafi kyawu da sauransu babu wanda ya halacci taron.

Duniya tana kallon wannan abin a matsayin fashin da makami dangane da kyautar akan danwasan na Real Madrid.

Rashin zuwan mahukuntan na Madrid taron hakan yasa armashin taron ya ragu inda mafiya yawan masu bibiyar kwallon kafa suka yi Allah wadai da wannan lamari.

An hago mafiya yawan ‘yan wasan Real Madrid suna saka hoton da suka taba rungumar danwasan nasu wato Vinicius a shafukan Instagram suna nuna alamar rarraahi a gareahi akan yayi hakuri akan wannan abu dayafaru wanda kowa ya shaida an tafka abin kunya.

Saidai wanda ya lashe kyautar wato Rodri ya zamo danwasa na biyu da ya fito daga gasar Premier ta kasar Ingila da ya lashe kyautar tun bayan Cristiano Ronaldo a shekarar 2008.

A hannu guda kuma kasar Vinicius wato Brazil ta bayyana cewar sabo da wariyar launin fata shiyasa aka hana danta wannan kyauta sabo da shi baki ne.

Daga karshe danwasan da ya rasa wannan kyauta yace zai rubanya kokarinsa har gida 10 suyi yadda suka ga dama da kyautar su tunda abin son zuciya ne.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?