Home » Mabarata Sun Hada Wike Da Allah Kan Hanasu Bara

Mabarata Sun Hada Wike Da Allah Kan Hanasu Bara

by Mubarak Ibrahim Mandawari
0 comment

A ranar Litinin 28 ga Satumbar 2024  ake sa ran wa’adin da Ministan Abuja Nyesome Wike ya bai wa mabarata na su fice daga birnin zai ƙare.

Kungiyar masu buƙata ta musamman dake Arewacin Najeriya ta yi kira ga ‘ya’yan ta da su tashi da azumi don neman taimakon Ubangiji bisa umarnin na ministan Abuja.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki tun daga yan majalisar wakilai da Sanatoci da Sarakuna da suyi duba kan lamarin.

Shugaban ƙungiyar ta masu buƙata ta musamman na Arewacin Najeriya, Yarima Sulaiman Ibrahim, ya shaida wa mane ma labarai cewa, “ya kamata ministan ya sake yin duba kan hukuncin, duk da cewa abin da Ministan ya faɗa doka ne, amma baza mu hana doka yin aikin ta ba.

“Abinda muke buƙata shine a zauna damu a kuma duba matsalolin mu, sannan a gano dalilin da yasa muke yin barar, a samar da hanyar daƙile wannan matsalar.” a cewar Yarima.

Ya ƙara da cewa abinda suka fi buƙata shine ba wai a basu abin da zasu ci ba, ko kuma a basu Naira dubu ashirin a matsayin jari, mu na so a ji koken mu, inji shugaban ƙungiyar.

Matsalar barace-barace musamman a manyan titunan Arewacin Najeriya na neman zama ruwan dare, a baya hukumomi sunyi ƙoƙarin kawo ƙarshen bara ta hanyar kama mabaratan, amma hakan yaci tura .

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?