• Home  
  • Yadda wata tifa ta take mutum 2 a kan babur a Jos
- Babban Labari - Labarai

Yadda wata tifa ta take mutum 2 a kan babur a Jos

Mutum biyu sun rasa rayukansu bayan da wata tifa ta murƙushe babur ɗin haya da suke kai a Mahaɗar Infant Jesus da ke kan titin Rukuba, a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato. Da yammacin ranar Laraba ne lamarin ya faru a daidai lokacin da mazauna yankin ke komawa gidajensu bayan kammala […]

Mutum biyu sun rasa rayukansu bayan da wata tifa ta murƙushe babur ɗin haya da suke kai a Mahaɗar Infant Jesus da ke kan titin Rukuba, a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato.

Da yammacin ranar Laraba ne lamarin ya faru a daidai lokacin da mazauna yankin ke komawa gidajensu bayan kammala harkokin yau da kullum.

Wata ganau mai suna Joy Nankin ta shaida wa wakilinmu cewa direban babur ɗin hayar yana ɗauke da fasinjoji biyu ne lokacin da tifar da ke gudun wuce kima ta buge babur ɗin a mahadar.

Ta ce, “Lamarin ya faru cikin ƙanƙanin lokaci. Direban babur yana ƙoƙarin tsallaka mahadar ne sai tifar ta zo daga baya ta take su.”

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai