Home » ‘Yan Arewa mazauna Abia sun shiga tirka-tirka da gwamnatin jihar

‘Yan Arewa mazauna Abia sun shiga tirka-tirka da gwamnatin jihar

by Anas Dansalma
0 comment
‘Yan Arewa mazauna Abia sun shiga tirka-tirka da gwamnatin jihar

A kwanakin baya mu kawo muku yadda wasu mazauna Lokpanta da ke jihar Abia suka yi ƙorafi kan rushe musu kasuwa da gidajensu ba tare da an sanar da su dalilan hakan ba daga gwamnatin jihar.

Sai dai a wannan karon ‘Yan Arewa mazauna kasuwar dabbobi ta Umuchieze da ke ƙaramar hukumar Umunneochi ta jihar Abian sun musanta zargin da gwamnatin jihar ta yi na suna binne gawarwakin mutane a kewayen kasuwar.

Sun ce gwamnatin na ba da wannan dalili ne kawai domin korar su daga wurin da suke kasuwancinsu tun shekarar 2005.

A yayin da yake magana da manema labarai, gwamnan jihar, Alex Otti, ya ce a wani bincike da suka gudanar, sun gano gawarwakin mutane babu kai da aka binne da ma waɗanda tuni sun zagwanye a kasuwar da ke Lokpanta.

Gwamnan ya ce rahoton bincike na musamman ya tabbatar da cewa mafi yawan kuɗaɗen fansa da ake karɓa bayan sace mutane a kan kawo ne a ajiye a kusa da kasuwar.

Wannan dalili, a cewar gwamnan, ya sanya musu fargaba game da yuwuwar ƙaruwar matsalar tsaro a wannan yanki inda kasuwar take saboda tuni wurin ya fara zama wani sansani na masu aikata laifuka da masu garkuwa da mutane.

Gwamnan ya ce sun umarci mazauna wurin da su daina kwana a kasuwar tare da komawa cikin al’ummar da ke kusa da su.

Sai dai mai magana da yawun ‘yan Arewa mazauna wannan kasuwa, Buba Abdullahi, ya nuna rashin amincewarsu da wannan mataki da gwamnan ya ɗauka.

Ya kuma ƙaryata zargin da gwamnan ke yi na akwai gawarwakin mutane a zagye da kasuwar kuma wai kasuwar ta zama sansanin ‘yan ta’adda.

Sannan ya zargi gwamnan da yunƙurin ƙwace musu gidaje waɗanda tuni aka fara rushe da yawa daga cikinsu.

Ya kuma ce mutane dubu goma 15 ne zaune a wannan wajen kuma gwamnatin tsohon gwamnan Orji Kalu ce ta ba su kyautar filin mai girman hekta 80.

A cewar malam Buba, matuƙar dai gwamnati za ta rushe musu gidaje tare da umartarsu da su koma cikin ƙauyukan da ke yankin, to tamkar gwamnatin na ƙorar su ne daga jihar ta Abia.

Sannan ya ce ‘yan Arewa na son zaman lafiya wanda hakan ne ya ba wa ‘yan Kudu dama su zauna a Arewa su yi kasuwanci ba tare da wani ya tsangwame su ba.

Ya ce babu adalci, idan wani ko wata suka yi ƙoƙarin hana wani ɗan Najeriya damar zama a kowanne yanki na ƙasar nan.

A ƙarshe ya roƙi gwamnatin da ta ƙyale ‘yan kasuwa su cigaba da zamansu a kasuwar, inda ya ce kuskure a ce su koma cikin al’ummar ƙauyukan Umuchieze, la’akari da ƙaruwar laifuka a yankunan.

Tare da tabbatar wa da gwamnati yunƙurinsu na haɗa kai da gwamnati wajen samar da mafita mai ɗorewa ga matsalar tsaro da ake fama da ita a ko’ina a Najeriya.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi