• Home  
  • Yan Banga Da Wasu Mutane 19 Sun Rasu A Yayin Arangamarsu Da Yan Bindiga A Yankin Da Gwamnan Bauchi Ya Fito.
- Babban Labari - Labarai

Yan Banga Da Wasu Mutane 19 Sun Rasu A Yayin Arangamarsu Da Yan Bindiga A Yankin Da Gwamnan Bauchi Ya Fito.

Daga Muazu Hardawa, Bauchi Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da kai mummunan harin Yan bindiga kan wasu Yan banga da mutanen kauyukan karamar hukumar Alkaleri Yankin da Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir ya fito. Harin da ake kyautata zaton ‘yan bindigar sun kaii a wasu kauyukan gwana ya kai ga kashe wasu mutanen gari […]

Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da kai mummunan harin Yan bindiga kan wasu Yan banga da mutanen kauyukan karamar hukumar Alkaleri Yankin da Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir ya fito.

Harin da ake kyautata zaton ‘yan bindigar sun kaii a wasu kauyukan gwana ya kai ga kashe wasu mutanen gari da Yan sintiri a kalla 19 nan take, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Kauyukan da aka kai harin na gundumar Gwana ne da ke karamar hukumar Alkaleri kamar yadda rahotanni daga yankin suka bayyana cewa kauyukan da aka kai harin sun hada da Mansur, Digare da Sabuwar Sara da kuma Yalo, Kuma an kai harin ne da yammacin ranar asabat inda aka kashe mutane akalla 19 tare da jikkata wasu da dama.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bauchi Sani-Omolori Aliyu ya ziyarci inda ta’asar ta abku domin gudanar da bincike a kan lamarin, Kuma ya tura ƙwararrun jami’ai don ci gaba da bin sawu da binciken ‘Yan Ina da kisan.

A lokacin da ya ke Alkaleri, kwamishinan ‘yan sandan ya tattauna da masu ruwa da tsaki, sannan ya bukaci kowa ya kwantar da hankalinsa, ya kuma baiwa ‘yan sanda goyon baya domin ci gaba da samar da tsaro kamar yadda ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike, musamnan ganin lamarin ya dauki sabon salon salwantar da rayukan bayin Allah.

A cewer Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, a wata sanarwa da ya fitar a makon da muke ciki, ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan ya yi Allah wadai da kashe-kashen, tare da nuna alhininsa kan hasarar rayuka da aka yi sakamakon wannan mummunan hari.

Rundunar ta umurci wata tawaga ta musamman da ta kara zage damtse wajen ganin an kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki da kuma mutanen da su ke da alaka da duk wani ta’addanci da ake yi a Yankin na Alkaleri da sauran sassan jihar Bauchi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000