Al’ummar garin Wailare a karamar hukumar Makoda ta jihar Kano, sun koka kan zargin da ake yiwa da wani mai suna Abdussalam Dandukulle, da daure kaninsa mai suna Basiru Dankiri da Sarka, tsawon shekaru da dama don ya mallaki gadonsa da aka raba musu.
Wasu dai sunce kusan shekaru 4 kenan matashin yake tsare a cikin wani daki wanda bashi da kulawar data kamata domin ko abincin kirki baya samu.
Sai dai wasu sun shaidawa, MUHASA TVR, cewa daman Basiru Dankiri, bashi da lafiya kuma ya shafe kusan shekaru goma.
- An Kama Hon Gudaji Kan Zargin Karɓar Kyautar Miliyan 70 Daga Emefiele
- Dan Majalissar Bagwai Da Shanono Ya Nemi Karin Jami’an Tsaro Kan Hare-haren Yan Bindiga A Mazabarsa
Dagacin garin Wailare, Alhaji Badamasi Halliru, ya bayyana cewa yaron bashi da lafiya shekarun baya da suka gabata, amma bai san halin da yake ciki ba a yanzu , har sai da ya samu labarin cewa an daure shi da sarka ba tare da kulawa ba.
Badamasi Halliru, ya kara da cewa yaje har gidan kuma ya ganewa idonsa inda ya ganshi cikin yanayi mara dadi koda jikinsa babu suturar kirki, inda suka yanke shawarar kai shi asibiti don kula da lafiyarsa.
Ya ce bisa shawarar da suka yanke ita ce za a siyar da gonar wanda aka daure din, don kai shi asibiti a kula da shi kamar yadda wasu yan uwansa suka amince kuma za a dinga rubuta duk abinda aka kashe a cikin kudin.
Wanda ake zargin , Abdussalam Dandukulle , ya musanta zargin da cewa harkar shaye-shaye ce ta jefa dan uwannasa cikin wannan larula, kuma shi da kansa ya kai shi asibitin Dawanau har ya samu lafiya.
Dandukulle ya kara da cewa maganar da ake yi akan takaddamar rabon gado ce ta sanya ya daure dan uwansa da sarka batun ba haka yake ba, domin su duk abunda suka yi masa sun yi masa saboda Allah ne harda kudin maganin da suka yi masa abaya.
Dagacin Garin Wailare, Alhaji Badamasi Halliru, ya shaida wa wakilin mu Mujahid Wada Musa , cewa sunje da safiyar yau Alhamis don kai matashin Asibiti, amma wata tsohuwar mata, ta hana a dauke shi, inda ta rufe gidan shi kuma yayansa da ake zargi ya yi tafiyarsa.
Haka zalika Dagacin ya tabbatar da cewa zargin da ake yiwa, Abdussalam Dandukulle, na neman ya mallake gadon kaninsa zai iya tabbata, domin alamun sun fito kara cewa baya son dan uwannasa ya samu lafiya yafi so ya mutu ya mallake dukiyar kamar yadda mutanen garin suke zargi.
Abdussalam Dandukulle da ake zargi ya mayar da martani da cewa lokacin da wata tsohuwa taje ta hana a fito dashi bayanan, har ta yi ikirarin cewa idan ma an yi masa magani ya warke wai tabarwa maigari gidan da ya gada.
Kan halin rashin tabbatas na kin bari a fito da Basiru Dankiri, don kai shi asibiti, dagacin ya ce yanzu haka yana kan kokarin rubuta takadda don sanarwa da jami’an yan sandan karamar hukumar Makoda don daukar mataki na gaba.
Wakilin mu ya kwashe kwanaki 9 yana gudanar da bincike tare da tuntubar dukkanin bangarorin da lamari ya shafa kafin wallafa labari.
A Shekarun baya-bayannan ma an samu makamantan hakan a jahohin Kano, Bauchi, Sokoto da Legas, inda wasu iyaye suka daure yayansu da sarka saboda wata bukata tasu har sai da jami’an yan sandan jahohin suka shiga cikin lamarin tare da fito da wadanda aka daure din cikin mummunan yanayi na rashin kulawa.