A karshe ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da mutane 85 a ƙauyen Wanzamai da ke cikin ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara sun amince su karɓi Naira 20,000 kan duk mutum ɗaya.
Sun kuma buƙaci hukumomi da su janye sojoji daga kauyen a matsayin wani ɓangare na sharuɗan sakin wadanda aka sace.
Sun ba da karfe 12 na daren jiya a matsayin wa’adin da suka ɗiba tare da yin barazanar kashe duk wanda ya kasa biyan kuɗi a kan lokaci ko kafin lokacin da aka kayyade.
Manema labarai sun tabbatar da cewa ‘yan bindidar sun yi barazanar cewa muddin ba a janye sojojin da aka tura ƙauyen Wanzamai ba za su ci gaba da yin garkuwa da mutanen ƙauyen.
Wani ɗan asalin yankin, Abubakar Na’Allah ya shaidawa manema labarai cewa, a wata tattaunawa ta wayar tarho ‘yan bindigar sun aike da sakon cewa za su karbi Naira 20,000 kacal daga kowane mutum a cikin mutane 85 da suka yi garkuwa da su a matsayin kuɗin fansa, la’akari da matsalar rashin kuɗi da suke ciki.
Na’Allah ya ce, “Tun da farko ‘yan fashin sun bukaci a biya su Naira miliyan 50 domin su sako mutane 85 da suka yi garkuwa da su wadanda galibinsu mata ne da kananan yara da suka je dajin neman ita ce a ranar Juma’ar da ta gabata.
Amma bayan tattaunawar da aka yi da su ne suka yi wannan ragi, saboda sun fahimci cewa dukkansu marasa galihu ne.