Rundunar yan sandan jihar Kano da INEC sun yaba da yadda zaɓen cike gurbin majalisar dokokin Jihar Kano mai wakiltar Dawakin Kudu ke gudana cikin lumana.
Kwamishinan ’yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, tare da kwamishinan hukumar zaɓe ta INEC a Kano, Ambasada Zango Abdu, sun duba rumfunan zaɓe domin tantance tsaro da yadda ake gudanar da zaɓen.
Kakakin ’yan sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce kawo yanzu babu wata matsala da aka fuskanta, yayin da jami’an tsaro za su ci gaba da kasancewa a rumfunan zaɓe har zuwa kammala tattara da bayyana sakamako.
INEC ta kuma yaba wa jami’an tsaro da al’ummar Dawakin Kudu kan haɗin kai da bin doka da oda.
