• Home  
  • Yan Sanda Sun Kama Mai Safarar Alburusai A Jarkar Manja
- Babban Labari

Yan Sanda Sun Kama Mai Safarar Alburusai A Jarkar Manja

Jami’an yan sandan birnin tarayya Abuja, tare da hadin gwiwar kungiyar masu sufurin motocin haya ( NURTW) sun samu nasarar kama Alburusai 488 da aka boye su a cikin jarkar Manja. Mukaddashin kwamishinan yan sandan birnin tarayya Abuja, mai kula da aiyuka na musamman, DCP Ishaku Sharu, ne ya tabbatar da hakan a lokacin da […]

Jami’an yan sandan birnin tarayya Abuja, tare da hadin gwiwar kungiyar masu sufurin motocin haya ( NURTW) sun samu nasarar kama Alburusai 488 da aka boye su a cikin jarkar Manja.

Mukaddashin kwamishinan yan sandan birnin tarayya Abuja, mai kula da aiyuka na musamman, DCP Ishaku Sharu, ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake holen wanda ake zargin a ranar litinin.

DCP Ishaku, ya ce an kama shi ne a tashar mota, dauke da harsasai 488 na bindiga kirar AK47 da aka boye a cikin Jarkar Manja.

Wanda ake zargin ya shaida wa jami’an yan sandan cewa ya karbo makaman a wajen wani mutum dake jihar Nasarawa, don kaiwa wani mai suna Yakubu Kachalla mazaunin Huntuwa ta jihar Katsina, bayan ya biyashi naira dubu 100,000.

Rundunar yan sandan ta ce wanda ake tuhumar yana bata hadin kai a ciga da tambayoyin da ake yi masa  kuma da Zarar an kammala za a gurfanar dashi a gaban kotu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai