Home » NIDCOM Ta Ceto Yan Nijeriya 956 Daga Gidan Yarin Libiya

NIDCOM Ta Ceto Yan Nijeriya 956 Daga Gidan Yarin Libiya

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

 

Daga : Abubakar Abdulkadir Kurawa

Hukumar da ke kula da ‘yan Nijeriya mazauna Ƙasashen Ƙetare (NIDCOM) ta ce an kuɓutar tare da mayar da ‘yan Nijeriya 956 daga gidajen yarin kasar Libya a cikin watanni ukun farko na shekarar 2025.

Hakan ya biyo haɗin gwiwar da hukumar NIDCOM ta samu tare da hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta duniya (IOM) a Nijeriya da kuma ofishin hukumar kula da baƙin haure da kuma wadanda rikici ya raba su da matsugunansu ta (NCRMI), a cewar sanarwar da hukumar NIDCOM ta fitar a ranar Litinin.

Jimillar ‘yan Nijeriya da aka mayar da su a cewar shugabar hukumar Hon. Abike Dabire –Erewa sun hada da mata 683, da maza 132, da yara 87 da kuma jarirai 54.
Sanarwar ta kara da cewa, an kasafta matakin dawo da ‘yan ƙasar kashi-kashi daga watan Janairu zuwa Maris din 2025.

Ma’aikatan VOA Sun Maka Shugaba Trump A Kotu

A ranar 28 ga watan Janairu an mayar da jimillar mutum 152 yayin da a ranar 11 da 19 da kuma 25 ga watan Fabrairu aka mayar da mutum 484, sai kuma a ranar 4 da 18 ga watan Maris Hukumar NIDCOM ta ce na an mayar da ‘yan kasar 320.
Kana a shekarun baya, fiye da ’yan Nijeriya 15,000 ne gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar hukumar kula da harkokin shige da fice ta duniya suka mayar da su gida.

Kazalika, Dabiri-Erewa ta jadadda kiran da hukumar ke yi wa ‘yan Nijeriya kan su guji balaguro zuwa kasashen waje ta ɓarauniyar hanya mai cike da haɗari kamar Libya, kasar da yaki ya ɗaiɗaita take kuma fama da tarin ƙalubale.
“Saboda yanayin siyasar Libya, muna gargadin ‘yan Nijeriya da su guji Libya a matsayin hanyar zuwa Turai, ba Libya kadai ba, har ma da sauran hanyoyin da ba su dace ba,’’ a cewar shugabar ta NIDCOM.

Ta kuma bukaci ‘yan Najeriya da su bi hanyoyin da doka ta tanada na yin hijira, inda ta yi nuni da cewa wasu ‘yan kasar da aka ceto daga Libya sun sake komawa Libya ko kuma su bi ta hanyoyin da suka fi hatsari don shiga Turai.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?