• Home  
  • Yan Sanda Sun Kama Masu Aikata Laifuka 105 Da Miyagun Kwayoyi Na Miliyoyin Naira A Kano
- Babban Labari - Labarai

Yan Sanda Sun Kama Masu Aikata Laifuka 105 Da Miyagun Kwayoyi Na Miliyoyin Naira A Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta kama wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka su 105 cikin watan satumbar nan , cikinsu harda wasu tarin kayan maye da aka samu nasarar kamawa wadanda ake zargin za a sha don aikata laifi. Kwamishinan yan sandan jihar CP Ibrahim Adamu Bakori ne ya gabatar da kayayyakin da […]

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta kama wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka su 105 cikin watan satumbar nan , cikinsu harda wasu tarin kayan maye da aka samu nasarar kamawa wadanda ake zargin za a sha don aikata laifi.

Kwamishinan yan sandan jihar CP Ibrahim Adamu Bakori ne ya gabatar da kayayyakin da aka kama ga manema labarai a yau.

Kwamishinan ya ce , dakarunsu karkashin jagorancin baturen yan sandan Rijiyar Zaki, SP Jamilu Bala sun yi nasarar kama Fatiki 603 na kwayar Tramadol wadanda darajarsu ta kai naira miliyan sittin da dubu dari uku ( 60,300,000) da kuma kwalaye 6 na kwayar Pregabalin wanda kudinsu ya kai naira miliyan ashirin da biyu da dubu dari hudu da ashirin da biyar ( 22, 425,000).

Wadanda ake zargin sun hada da yan fashi da makami 17, masu safarar miyagun kwayoyi su 8, barayin motoci 9 da masu satar Adaidata sahu 5 da yan Daba 57da sauran masu sace-sace 9.

Sauran kayayyakin da aka kwato sun hada da bindigu kirar AK-47 guda 3, bindigu kirar Pistol guda 3, bindigu kirar Revolver guda 3, bindiga kirar gida AK4-7 guda 1, Bindiga Doguwa kirar gida 1 da bindigu gajeru kirar gida guda 2.

Sauran sune albusai 7 da kwanson harsasai guda 5 wadanda aka yi amfani da su.

Haka zalika an kwato baburan adaidata sahu na sata guda 2, Babura 13 da shanu guda 3 da kuma motoci guda 7.

Kwamishinan ya kara da cewa an kwato takubba 38,Adduna 42, Wukake 58 da sauran karafa 31.

 

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai